TSAKURE
Wannan takarda ta yi tattaki ne wajen yin tsokaci a kan irin gudunmawar da Fassara da Baddala suka bayar ga samuwar rubutun zube na Hausa. Takardar ta nuna gudunmawar ne ta tsarin mataki-mataki har guda huxu, wato ta yadda ya kasance daga wannan qarni zuwa wancan. Har ila yau takardar ta wajen yin amfani da waxannan matakan ta kawo misalai na litattafai na addini da ilimi da waqoqi da labarai da kuma was an kwikwayo, a qarshe takardar ta kamala da bayar da wasu yan shawarwari